Wikipedia:Kofan al'umma
- Sannun ku da zuwa Kofan al'umma. Wannan shafi ne na tattaunawa akan Hausa Wikipedia baki ɗaya da kuma abubuwan da suka shafi inganta ta. Sannan anan ake bada sanarwa ko wani saƙo da ya shafi dukkan Wikipedia ko ake buƙatar ya isa ga kowane mai bada gudummuwa
- Archives: Tattaunawar da aka yi daga 2005 zuwa 2017.
- Tarihi: Tattaunawar da aka yi daga 2023 zuwa yau.
Buƙatar Sake Amincewa da Ni a Matsayin Admin
[gyara masomin]Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.
Bayan cikar wa’adin watanni shida na hidimatawa a matsayin Admin na Hausa Wikimedians User Group kamar yadda tsarin ƙungiya ya tanada, ina miƙa buƙatata ga al’umma domin a sake duba yiwuwar ba ni wannan dama na wani sabon zango.
Ina da ƙuduri da niyyar ci gaba da ba da gudummawata domin bunƙasa Hausa Wikipedia tare da kiyaye gaskiya, adalci da haɗin kai. Ina roƙon al’umma da su sake ba ni amincewa domin ci gaba da hidima. Na gode da lokacinku da kulawarku.
Muhammad Idriss Criteria (talk) 13:29, 2 ga Maris, 2026 (UTC)
Support
[gyara masomin]- @Muhammad Idriss Criteriana amince domin kawo cigaba a wikipedia Ibrahim abusufyan (talk) 15:03, 2 ga Maris, 2026 (UTC)
- na amince don ka cigaba da muhimmiyar aiki da ka faro wata shida da suka wuce. Allah ya kara basira da kwarin gwiwa Umar2z (talk) 17:07, 2 ga Maris, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya sosai, hakan ƙarin ci gaba ne a Hausa Wikipedia.Captain Pharouq 13:41, 2 ga Maris, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya sosai akan hakan. Wannan cigaba ne ga Hausa Wikipedia gaba ɗaya
Hauwau sulaiman (talk) 13:52, 2 ga Maris, 2026 (UTC)
- Ina goyon bata dari bisa dari Nnamadee (talk) 20:56, 2 ga Maris, 2026 (UTC)
Sanarwa da Neman Goyon Baya
[gyara masomin]Barka da wannan lokaci
Ina fatan kuna lafiya, zanyi amfani da wannan damar domin in sanar daku cewa muna shirin gudanar da campaign mai take "Wikipedia Pages Every Wikipedia should have", idan Allah ya yarda. Dan haka muke sanar daku tare da neman shawarar ku. Wannan campaign din zai kawo cigaba a ɓangaren ƙirƙira tare da inganta muƙalu da ake buƙata a Hausa Wikipedia. Nagode
Pharouqenr (talk) 05:43, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
- Support Allah ya bada nasara ya kuma sa a cimma manufa Muhdavdullahi (talk) 07:11, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
- Support Hakan na da Karanci dan haka wannan abu me kyau ne kwarai kuma muna goyon bayan Allah ya bada saa 105.112.206.75 09:18, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
- support Allah ya bada saa muna goyon baya
- Manaf205 (talk) 09:20, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
- Enah goyan bayanka Pharouqenr domin wanan campaign din zai kawo mana cigaba a Hausa Wikipedia Smshika (talk) 10:47, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
Support Hakika wannan wani ci gaba be muna goyan baya dari Bisa dari domin cigaban al'uumar wikipedia Baki daya Ibrahim abusufyan (talk) 07:38, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
Support hakan yayi kuma yana da kyau, Allah ya bada sa'a da nasara akai Mahuta (talk) 08:25, 27 ga Augusta, 2025 (UTC) Mahmud maby (talk) Support Hakika wannan wani ci gaba be muna goyan baya dari Bisa dari domin cigaan al'uumar wikipedia Baki daya mahmud maby (talk) 12:05 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
- Support Ina goyon bayan haka dari bisa dari domin zai kawo ci gaba sosae a Wikipedia Nnamadee (talk) 13:31, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
Support Ina goyon bayan yin hakan Allah ya tabbatar da alkhari. Muhammad Idriss Criteria (talk) 15:06, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
~~Ina goyan bayan hakan Allah ytabbatar da Alkairi~~
Hausa Community Streets vox pop campaign
[gyara masomin]Barkan kuda wannan lokacin. Ina mai farin cikin sanar daku cewa. muna shishirye shiryen kawo muku campaign Wanda zaiyi hira da mutanen arewacin nigeria akan yadda suka san Wikipedia da kuma yadda suma zasu fara gyara a cikinta. inda zaayi vidiyo din interview din a watsa a duniyar yanar gizo domin kowa ya gani kuma ya iya anfani dashi. a matsayina na content creator mai tasowa wannan damace sosai gamu hausawa baki daya. muna goyan bayanku zuwa wannan lokaci. mungode. Musa Vacho77 (talk) 08:04, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
- Muna goyon bayan wannan kamfe saboda shine na farko a wannan manhaja ta Hausa, hakika zai kawo cigaba ga jama'a. Patroller>> 07:39, 29 ga Augusta, 2025 (UTC)
Sanarwa da Neman Goyan baya Khalifah123 (talk) 11:50, 27 ga Augusta, 2025 (UTC)
WikiAcademics - Fadada Wikimedia a Jami'o'in Arewacin Najeriya
[gyara masomin]Assalamu alaikum,
Kungiyar Hadaka Open Learning Network tana jagorantar wani aikin tallafi na Wikimedia Community Fund mai taken WikiAcademics: Fadada Wikimedia a Jami’o’in Arewacin Najeriya".
Manufar aikin:
- Ƙarfafa ɗalibai da malaman jami’o’i su shiga aikin Wikipedia.
- Samar da horo da koyarwa domin bunkasa rubuce-rubuce a Hausa Wikipedia.
Cikakken bayani da aikace-aikace Na Nan.
Ku shiga, ku bada ra’ayi, ku taimaka wajen bunƙasa ilimi!
Hadaka Open Learning Network
Sanarwa da neman goyon baya
[gyara masomin]Assalamu alaikum yan uwa da abokan arziki editoci na Hausa Wikipedia. Ina mai farin cikin sanar da ku tare da neman goyon baya da shawarwari game da wani Rapid Grant mai taken Preserving Bauchi’s History and Culture Through Reliable Knowledge Creation on Wikimedia. da nake nema. Manufar wannan aiki ita ce tattara da rubuta tarihi da al'adu game da abinda ya shafi Bauchi da ta hanyar inganta tsofaffin muƙaloli da ƙirƙirar sabbin, bayanai, da hotuna a kan dandalan Wikimedia. Wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa tarihi da al’adun Bauchi sun samu tsari kuma sun kasance a bude ga kowa a duniya. Ibrahim Sani Mustapha (talk) 06:58, 28 ga Augusta, 2025 (UTC)
Wiki Green in Northern Nigeria: Documenting Hausa Native Plants On Wikimedia Commons Through Photo Walks
[gyara masomin]Assalamualaikum Ina maku Barka da wannan lokaci ƴan uwa editors da kuma shuwagabannin wannan manhaja ta Hausa Wikimedis tare da fatan kowa yana lafiya amin. Bayan haka, ina mai farin cikin sanar da ku cewa zamu shirya wani proposal mai taken:Wiki Green in Northern Nigeria: Documenting Hausa Native Plants On Wikimedia Commons Through Photo Walks da fatan zamu samu shawarwarin ku da kuma goyon bayan ku, harda ma gyare-gyaren ku. @M Bash Ne (talk) 08:19, 30 ga Augusta, 2025 (UTC)
Hausa Wiktionary Harmonization and Community Initiative Activities
[gyara masomin]Barkan mu,ina mai farin cikin gayyatarku zuwa wurin shirin dazamu gudanar na cigaban aikin mu dan habaka Hausa Wiktionary ta hanyar inganta kalmomi wanda ya kunshi daura hoto,daura Audio da wasu sabbin ayyuka ma kamar su Synonym da Anagrams.Abubakr1111 (talk) 23:20, 30 ga Augusta, 2025 (UTC)
- @Abubakr1111 An fidda lokaci da wuri? Pharouqenr (talk) 09:40, 3 Satumba 2025 (UTC)
- Yanzu hakadai project din yana under review,kome ake ciki zamu sanar daku nan gaba. Abubakr1111 (talk) 13:36, 3 Satumba 2025 (UTC)
- Ok nayi zatan har funding anyi, naji kace "gayyata". Na fahimta yanzu. Kamar neman goyon baya kenan ko? To Allah ya tabbatar da hakan ina goyon baya. Pharouqenr (talk) 13:40, 3 Satumba 2025 (UTC)
- Ga link din discussion page domin nuna goyon baya:https://meta.wikimedia.org/w/index.php?title=Grants_talk:Programs/Wikimedia_Community_Fund/Rapid_Fund/Hausa_Wiktionary_Harmonization_and_Community_Initiative_Activities_(ID:_23550226)&action=edit&redlink=1. Nagode Abubakr1111 (talk) 12:20, 4 Satumba 2025 (UTC)
- Ok nayi zatan har funding anyi, naji kace "gayyata". Na fahimta yanzu. Kamar neman goyon baya kenan ko? To Allah ya tabbatar da hakan ina goyon baya. Pharouqenr (talk) 13:40, 3 Satumba 2025 (UTC)
- Yanzu hakadai project din yana under review,kome ake ciki zamu sanar daku nan gaba. Abubakr1111 (talk) 13:36, 3 Satumba 2025 (UTC)
Sanarwa akan biki zagayowar shekara ta wikidata
[gyara masomin]Barkan mu da war haka.
Ina mai farin chikin sanar da jama'ar wannan tafiya ta wikipedia Hausa cewa muna kokarin kaddamar da bukata na neman tallafi don gudanar da wayar da kai akan wikidata a Adamawa da kuma Nasarawa dafatan Allah ya bamu nasara Amin. Umar2z (talk) 01:48, 31 ga Augusta, 2025 (UTC)
Wikipedia Voice For All
[gyara masomin]Barkan ku da wannan lokacin. Inama editocin Hausa fatan Alkhairi. nazo na sanar daku cewa muna shirye shiryen kawo muku campaign na mata a Wikipedia Hausa saboda haryanzu mun rasa kwararrun editoci mata a shafin mu, wanda idan muka duba wasu shafin Wikipedia zamuga yadda mata suke taka rawar gani sosai. da fatan wannan taro namu me taken Wikipedia Voice For All zai kawo cigaba ga matan mu editors. nagode Galdiz (talk) 22:59, 3 Satumba 2025 (UTC)
- Support
Ina goyon bayan wannan shirin saboda karfafa mata akan ayyukan Wikipedia da kuma samun kwararrun editoci mata da masu wakilci ta bangaren mata. Allah ya bada Sa'a. Jidda3711 (talk) 21:06, 6 Satumba 2025 (UTC)
Support Ina goyon bayan wannan yunƙuri na karfafa muradin mata da bayyana tarihin su a Wikipedia. Na jima da ganin yadda gudummawar mata ke ƙaranci a cikin babbar kundin ilimi na duniya. Lokaci ya yi da za a gyara hakan. Allah ya Bada sa'a Saudarh2 (talk) 21:03, 6 Satumba 2025 (UTC)
Global discussion on Welcome messages
[gyara masomin]MediaWiki message delivery (talk) 02:38, 13 Satumba 2025 (UTC)
- Thank you for reaching out, the welcome messags sent by new user have Tutorials on it, for new users it's better for them know how to edit on our Wiki first before practicing it in order to avoid violations.
- Thank you @MediaWiki message delivery for reaching out. The welcome messages sent to new users contain tutorials. For new users, it's better for them to learn how to edit on our wiki first before practicing, in order to avoid violations. Captain Pharouq 09:29, 13 Satumba 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Murnar zagayowar Shakarar Wikidata a Gombe Network
[gyara masomin]Assalamu alaikum
Muna farin cikin sanar da ku cewa Gombe Network zata yi murnar zagayowar shekarar wikidata ta goma sha uku, kuma muna so mu yi amfani da wanna rana don fassara abubuwan wikidata zuwa yaren Hausa. Muna neman fatan alkhairi da kuma shwawarwari daga wannan alummah mai albarka. mun gode Umar2z (talk) 17:00, 15 Satumba 2025 (UTC)
Mai sauya uwar garken - Za a karanta wiki-kawai na ɗan gajeren lokaci nan ba da daɗewa ba
[gyara masomin]Karanta wannan saƙon a wani yaren • Kuyi ƙoƙarin fassara wannan saƙo zuwa Hausa
Wikimedia Foundation za'a gwada chanji tsakanin cibiyoyin bayanai na farko dana sakandare. Wannan zai tabbatar da cewa Wikipedia da sauran wikis na wikimedia na iya tsayuwa akan yanar gizo koda bayan wata ruɗani
Duk zirga-zirga za su kunna 24 Satumba. Gwajin zai fara daga karfe 15:00 UTC.
Abin takaici, saboda wasu iyakoki na cikin MediaWiki, dole a dakata da duk gyararraki dole ne a yayin da muke yin sauyin. Muna neman afuwa game da wannan tsaiko, kuma muna aiki don raguwarsa nan gaba.
Za a nuna wata tuta a kowace wikis mintina 30 kafin wannan aikin ya faru. This banner will remain visible until the end of the operation. You can contribute to the translation or proofreading of this banner text.
Zaka iya karantawa, amma banda gyara, a duka wikis na wani ɗan ƙanƙanin lokaci.
- Ba za ku iya yin wani gyara ba har na tsawon awa ɗaya a ranar Laraba 24 Satumba 2025.
- Idan kayi ƙoƙarin gyara ko ajiyewa awannan lokacin, zaku ga saƙon kuskure. Muna fatan cewa babu gyara da za ayi asara awannan lokacin, amma ba za mu iya tabbatar muku ba. Idan ka ga sakon kuskuren, to don Allah a jira har komai ya koma daidai. Sannan ne zaku samu damar adana gyaran ku. Amma, muna ba da shawara cewa ku kwafe canje-canjen ku tun daga farko, idan da hali.
Wasu sakamakon:
- Ayyukan bango zasu Kasance a hankalu kuma wasu za'a iya ajiye su. Tana iya kasancewa hanyoyin hadin masu kalar-ja ba zasu dawo ba da sauri kamar yadda aka saba. Idan ka kirkiri labarin da aka riga aka danganta shi a wani wuri, hanyar hadi zata zauna a kalar-ja fiye da yadda aka saba. Dole ne a tsaida duk wasu rubutuka masu daɗewa
- Muna sa ran tura lambar za ta faru kamar kowane mako. Koyaya, wasu daskarewar lamba-by-case na iya faruwa akan lokaci idan aikin ya buƙaci su daga baya.
- GitLab ba zai kasance ba na kusan mintuna 90.
Ana iya jinkirta wannan aikin dangane da yadda hali ya bada Za ka iya karanta tsarin a read the schedule at wikitech.wikimedia.org. Za a sanar da duk wanu canji na wannan jadawalin.
Ayi kokarin yadda wannan bayanin tare ga jama'ar ku.Trizek (WMF) (Tattaunawa) 15:41, 18 Satumba 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Neman Ci Gaba Da Zama Mai Gudanarwa
[gyara masomin]Assalamu alaikum yan’uwa masu bada gudunmawa a shafin Hausa Wikipedia. Hakika ina daga cikin masu gudanarwa (administrators) a shafin Hausa Wikipedia, kuma ga shi wa'adin gudanarwata yana dab da ƙarewa, hakan ta sanya make fatan ci gaba da wannan aiki domin kula da tsari, tsafta, da kuma kare wannan shafi daga duk wani abin da zai iya kawo cikas ga ci gabansa. Saboda haka nake neman goyon bayan ku da amincewar ku domin in ci gaba da zama mai gudanarwa (administrato). Goyon bayan ku da shawarwarin ku suna da matuƙar muhimmanci a gare ni da kuma al’ummar Hausa Wikipedia gaba ɗaya. Na gode. A Sulaiman Z (talk) 22:42, 26 Satumba 2025 (UTC)
- :Ina bada goyon baya dari bisa dari Gwanki(Yi Min Magana) 05:35, 27 Satumba 2025 (UTC)
- :Support Ina mai bayyana goyon bayana a bisa ci gaba da kasancewrsa admin a Hausa Wikipedia. A'isha A Ibrahim (talk) 13:40, 27 Satumba 2025 (UTC)
- Support hakika ka kasa ce edita mai bada gudummawa sosai a Hausa Wikipedia, dan haka sake baka wannan damar wata babbar nasara ce ga shafin Hausa Wikipedia na bunƙasa shi, dan haka ina goyon baya Mahuta (talk) 04:54, 27 Satumba 2025 (UTC)
- Support Tabbas Ina goyon bayan ka sake kasancewa Admin a karo na biyu. Muhammad Idriss Criteria (talk) 07:52, 27 Satumba 2025 (UTC)
- Support Ina goyon baya sosai domin cigaba da kula da ayyukan editici da kuma kawo cigaba wajan gyara ayyukan da suka saɓa ƙa'ida. Captain Pharouq 12:11, 27 Satumba 2025 (UTC)
- Support Ina matukar goyon bayan wannan shawara ta sake zama Admin a Hausa Wikipedia,sabi da ka kasance cikakken mai bada gudunmawa a Wikimedia baki daya don haka ina goyon bayan.Ibrahim Sani Mustapha (talk) 13:16, 27 Satumba 2025 (UTC)
- Lallai wannan edita jajirtaccen ne wurin bada gudunmawa a wannan shafi na Wikipedia da sauran ƴan uwanta, ina goyon bayan ya ci gaba da kasancewa mai gudanarwa a wannan shafi Support Hamza DK (talk)
- Ina goyan bayan samun wannan dama a karo na biyu. Hakan karin jawo cigaba ne ga Hausawa Wikipedia. BnHamid (talk)
- Support ina goyan bayan ka dan sake zama Admin saboda irin gudummawar da kake bayarwa.Galdiz (talk) 05:20, 3 Oktoba 2025 (UTC)
- Ina bada goyan baya akan ka zama mai gudanarwa saboda irin jajircewa da kuma gudunmawa da kake badawa a manhajar Wikipedia musamman a bangaren yaren Hausa. Captain1044 (talk) 11:46, 4 Oktoba 2025 (UTC)
Neman Goyon Bayan Zama Mai Gudanarwa (Administrator)
[gyara masomin]Salam, Dafatan kuna lafiya Yan uwa. ina mai neman goyon bayanku. na kasance mai gyara gyare a Wikipedia musan man ta Hausa tun 2019. inada sha'awar gyare gyare musan man akan abunda ya shafi ka'idojin rubutu, gaba dake tsakanin rubutu, saka manazarta da kuma gyara fassarori zuwa ga tabbacciyar ingantaciyar rubutu wanda za'a iya karantawa. Ina neman goyon bayanku. nagode. Musa Vacho77 (talk) 13:15, 2 Oktoba 2025 (UTC)
- Strongly Support SS Omoty77 (talk) 04:09, 3 Oktoba 2025 (UTC)
- Gaskiya enah goyon bayan Musa Vacho77 kazama Admin sabo da ɗadewan da kayi kana bada gudunmawa a Hausa Wikipedia Smshika (talk) 07:05, 7 Oktoba 2025 (UTC)
- Support, ƙwararren edita ne kuma yana da kishi. Ina goyon bayan zaman sa admin.
- Strongly Support SS Omoty77 (talk) 04:09, 3 Oktoba 2025 (UTC)
- Gwanki(Yi Min Magana) 18:53, 3 Oktoba 2025 (UTC)
- Walaikumus Salam ɗan uwa. Ni Umar-askira ina goyon bayan wannan editan ya zama admin a Hausa Wikipedia. Fatan alkhairi Umar-askira (talk) 13:34, 4 Oktoba 2025 (UTC)
- Support Ina go yan baya dari bisa dari. Saboda mun yaba da yanda yake jajircewa wajen wayan ma sababbin editors Kai da kuma basu gudun mawa wajen basu Illumin da yakamata wajen yin ingan tacen editing yada yakamata.
(Abubakar Yusuf Gusau (talk) 20:33, 2 Oktoba 2025 (UTC))
- Support Gaskiya ina goyon bayan ka dan zama Admin dari bisa dari domin gudummawar da kake badawa a wikipedia.Galdiz (talk) 04:25, 3 Oktoba 2025 (UTC)
- Support Tabbas wannan babban edita ya cancanci ya zama edita domin ya daɗe yana bada gudummawa a shafin Hausa Wikipedia, sannan yana da gurin bunƙasa maƙalolin shafin Hausa Wikipedia, bashi wannan damar wata babbar nasara ce gare mu baki ɗaya na cigaba da bunƙasa shafin Hausa Wikipedia, dan Haka ina goyon baya Mahuta (talk) 05:41, 3 Oktoba 2025 (UTC)
- Support ƙwararren edita ne da ya daɗe yana bada gudummowa. Ina goyon bayan zaman sa admin.Abubakr1111 (talk) 11:00, 4 Oktoba 2025 (UTC)
- Samfuri:S Tabbas Hausa Wikipedia na bukatan kwararrun editoci wanda suka dade suna bada gudummawa da jajircewa wajen kawo cigaba a wannan shafi. Saboda haka ina goyon bayan haka.Patroller>> 11:21, 4 Oktoba 2025 (UTC)
- Support Ina goyan bayan bama wannan editan admin ganin dacewar shi da kuma dadewar shi yana bada gudunmawa
- Sadauki11 (talk) 14:20, 6 Oktoba 2025 (UTC)
Neman Zama Admin karo na biyu
[gyara masomin]Assalam, da fatan kuna lafiya. Ina mai neman goyon bayanku akan sabunta wa'adin zama Admin a karo na biyu domin kula da nagartaccin ayyuka da kuma tankaɗe ayyuka masu kyau. Nagode.. Bissalam.
Captain Pharouq 13:36, 7 Oktoba 2025 (UTC)
- Support ina mai goyon bayan haka 100% duba da irin koqsrin dakake na ganin an inganta muqalu da jajircewa gurin koyarda sabbin editors Muhdavdullahi (talk) 05:24, 8 Oktoba 2025 (UTC)
- Support Ina goyon bayan hakan sosai domin inganta hausa Wikipedia. Tabbas hakan zai kawo ci gaba Najeebbabi (talk) 13:42, 7 Oktoba 2025 (UTC)
- Support Ina goyon baya 100% domin jajirtaccen aikin da kakeyi a matsayin mai gudanarwa. Moherhh (talk) 13:47, 7 Oktoba 2025 (UTC)
- Support Ina goyon baya saboda jajircewa da kwazo na wannan edita.
- Support Aisha Yahuza (talk) 15:19, 7 Oktoba 2025 (UTC)Ina goyon bayan hakan saboda kwazo da jajircewa wannan editan
- Support Ina goyon bayan hakan dari bisa dari
- Support' Ina goyon baya Muhammad Idriss Criteria (talk) 15:51, 7 Oktoba 2025 (UTC)
- ’’’Support’’’ Ina Goyan bayan hakan Dari bisa dari saboda hazaka da jajircewar wannan editan
- Support: Tabbas ina goyon bayan sake kasancewarka mai gudanarwa saboda irin jajircewarka wajen ganin an tsaftace shafin Hausa Wikipedia daga dukkan wani koma baya. A Sulaiman Z (talk) 19:33, 7 Oktoba 2025 (UTC)
- Support support 100% Manaf205 (talk) 09:53, 8 Oktoba 2025 (UTC)
Ku fadi ra'ayinku: zaben 2025 Kwamitin Amintattu
[gyara masomin]Barkan mu,
Lokacin jefa ƙuri'a na 2025 Zaɓen Kwamitin Amintattu ya buɗe. 'Yan takara na neman kujeru biyu (2) a Kwamitin.
Don duba cancantar masu jefa ƙuri'a, da fatan za a ziyarci shafin cancantar masu jefa ƙuri'a.
Ƙara koyo game da su ta karanta bayanan aikace-aikacen su da kallon bidiyon takararsu.
Lokacin da kun shirya, ku je zuwa shafin zabe na SecurePoll don kada kuri'a.
Za a buɗe zaɓe daga 8 ga Oktoba a 00:00 UTC zuwa Oktoba 22 a 23:59 UTC.
Gaisuwa mafi kyau,
Abhishek Suryawanshi
Shugaba, Kwamitin Zabe
MediaWiki message delivery (talk) 04:48, 9 Oktoba 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Help us decide the name of the new Abstract Wikipedia project
[gyara masomin]Hello. Please help pick a name for the new Abstract Wikipedia wiki project. This project will be a wiki that will enable users to combine functions from Wikifunctions and data from Wikidata in order to generate natural language sentences in any supported languages. These sentences can then be used by any Wikipedia (or elsewhere).
There will be two rounds of voting, each followed by legal review of candidates, with votes beginning on 20 October and 17 November 2025. Our goal is to have a final project name selected on mid-December 2025. If you would like to participate, then please learn more and vote now at meta-wiki. Thank you!
-- User:Sannita (WMF) (talk) 11:42, 20 Oktoba 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Sanarwa tare da neman goyon baya
[gyara masomin]Ƴan'uwa masu daraja dafatan kuna lafiya, inaso nayi amfani da wannan damar domin na shaida maku muna shirin gudanar da taron Wiki Loves Africa 2026 In Kebbi and Niger insha Allah, muna neman goyon bayan ku tare da haɗin kai da kuma shawarwarin da kuke ganin ya dace nagode. Mahuta (talk) 04:55, 21 Oktoba 2025 (UTC)
Kakaranta muƙalar da ƙyau kafin ka wallafa ta
[gyara masomin]Assallamu'alaikum malam Mahmud maby Sannu da ƙokari kalura da abin da kake fassarawa kafin ka wallafa, wanan muƙalan mai suna Labarin inganci abinci na Tarayyar Turai: Tarihin sauye-sauyen bata da Ma'ana ko ƙadan kaje ka inganta ta dan Allah in koma baga inganta ta ba zan gogeta nan da kwana biyu nagode Smshika (talk) 14:00, 22 Oktoba 2025 (UTC)
Wikifunctions will be deployed on your wiki on 2025-11-05
[gyara masomin]Hi all, we want to let you know that Wikifunctions is coming to your project soon! When enabled, you will be able to call functions from your project, and integrate them in your articles.
A function is something that takes one or more inputs and transforms them into a desired output. Think of adding up two numbers, or converting miles into metres, or calculating how much time has passed since an event, or declining a word into a case. This is usually done with templates that are complicated to create or to import. With Wikifunctions, you will be able to do this with just a couple of clicks!
Please check out these tutorials for more details. You’re also invited to create functions that you find useful, or ask for help from the Wikifunctions community.
We would like to invite you to contribute to Wikifunctions, by translating the existing functions labels into your language, so that more users in your community can more easily reuse them on the project. You can also translate the messages for the Wikifunctions interface on TranslateWiki (here for VisualEditor messages, and here for the Wikifunctions interface proper).
Of course, we are happy to help in case there are questions or difficulties, and we are ready to listen to your feedback. Please ping me directly in case of necessity or reach out to me on my talk page.
--Sannita (WMF) (talk) 12:22, 29 Oktoba 2025 (UTC)
- Hi all, unfortunately due to a technical problem we couldn't deploy Wikifunctions on your project. We will keep you updated about the next date of deployment. Thanks for your comprehension! Sannita (WMF) (talk) 13:57, 6 Nuwamba, 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Neman masu sa kai don shiga da dama daga cikin kwamitocin motsi.
[gyara masomin]Kowace shekara, yawanci daga Oktoba zuwa Disamba, da yawa daga cikin kwamitocin motsi suna neman sabbin masu sa kai.
Kara karantawa game da kwamitocin akan shafukansu na Meta-wiki:
Aikace-aikacen kwamitocin suna buɗe 30 Oktoba 2025. Aikace-aikace don Kwamitin Alaƙa, da kuma aikace-aikacen Hukumar Ombuds kuma Kwamitin Binciken Harka ya rufe 11 Disamba 2025. Koyi yadda ake nema ta ziyartar shafin alƙawari akan Meta-wiki. Aika zuwa shafin magana ko imel cst
wikimedia.org tare da kowace tambaya da kuke da ita.
Ga Tawagar Taimakon Kwamitin,
- MKaur (WMF) 14:12, 30 Oktoba 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Sanarwa da neman goyon baya ko shawara
[gyara masomin]Assalamu Alaikum,
Yan'uwa editocin Wikipedia, dafatan kuna lafiya, ina amfani da wannan damar domin na sanar da ku shirin mu na Wikipedia birthday @ 25 karkashin Kaduna Network, shirin zai taimaka wajen bunƙasa wasu daga cikin makalolin Hausa Wikipedia da sauran su, dafatan zaku bamu goyon baya da haɗin kai Halima Waziri (talk) 19:10, 30 Oktoba 2025 (UTC)
Duplicate articles
[gyara masomin]Hello, this would be entirely in English as I do not speak or understand Hausa. These two articles are about the same topic, and I think they could be merged together: Ganuwar Benin and Benin Moat. I will suggest merging the contents of Ganuwar Benin into Benin Moat or whichever works best. Pinging editors who I think could handle this, anyone else could: @Uncle Bash007, Muhammad Idriss Criteria, Gwanki, and Pharouqenr:
Thank you, and happy editing! Vanderwaalforces (talk) 07:18, 31 Oktoba 2025 (UTC)
- Thank you @Vanderwaalforces i have noticed it, and Ganuwar Benin is more reliable than Benin Moat. So i have deleted Benin Moat now. And thank you for reaching out and wishing you all the best.
- Captain Pharouq 07:30, 31 Oktoba 2025 (UTC)
- @Pharouqenr You could redirect Benin Moat to Ganuwar Benin, since it is more or less the English name, instead of nuking it entirely.
- Happy editing! Vanderwaalforces (talk) 07:31, 31 Oktoba 2025 (UTC)
Sanarwa, akan Zamar Karshen shekara a Gombe Network
[gyara masomin]Muna sanar da jama'ar mu chewa Wikimedia User Group Nigeria, Gombe Network, tana kokarin neman tallafi na gudanar da zaman karshen shekara don kara sanayya da fihimta game da shiryeshiryen mu na shekara mai zuwa Umar2z (talk) 21:36, 14 Nuwamba, 2025 (UTC)
Neman admin akaro na biyu
[gyara masomin]| Akwai goyon baya –Ammarpad (talk) 20:21, 22 Disamba 2025 (UTC) |
Wannan tattaunawar an rufe ta. Babu buƙatar a sake ƙara wani bayani a wannan sashin. Duk wani ƙarin bayani, za'a iya yin sa shafin da ya dace ko kuma a babban shafin Kofar al'umma. Ku tuna, babu buƙatar ƙara kowane irin bayani a wannan sashin.
Ina neman goyon bayanku domkn kasancewa admin akaro na biyu domin cigaba da tabbatar da ayyuka na gari da kuma bada gudumuwa ta hanyar taimakon editoci. Ibrahim abusufyan (talk) 10:52, 2 Nuwamba, 2025 (UTC)
Support
[gyara masomin]- Support Tabbas ina goyon baya sosai. Hakan zai kawo cigaba sosai a Wikipedia Captain Pharouq 11:07, 2 Nuwamba, 2025 (UTC)
- Support Haƙiƙa wannan edita ya kasance ɗaya daga cikin editocin dake ƙoƙarin bunƙasa shafukan Hausa Wikipedia, tabbas sake ba shi wannan damar wata babbar nasara ce ta cigaba da tsaftace maƙalolin dake Hausa Wikipedia tare da inganta su dan haka ina goyon baya. Mahuta (talk) 11:15, 2 Nuwamba, 2025 (UTC)
- Goyan baya Ina mai goyan bayan ba ka damar mai gudanarwa a karo na biyu, duba da hakan zai taimaka wajen kara kawo cigaba da ma tsaftace Hausa Wikipedia. BnHamid (talk)
- Ina Goyan bayan hakan Dari bisa Dari domin cigaban Wikipedia Khalifah123 (talk) 23:27, 2 Nuwamba, 2025 (UTC)
Reminder: Help us decide the name of the new Abstract Wikipedia project
[gyara masomin]Hello. Reminder: Please help to choose name for the new Abstract Wikipedia wiki project. The finalist vote starts today. The finalists for the name are: Abstract Wikipedia, Multilingual Wikipedia, Wikiabstracts, Wikigenerator, Proto-Wiki. If you would like to participate, then please learn more and vote now at meta-wiki. Thank you!
-- User:Sannita (WMF) (talk) 14:22, 20 Nuwamba, 2025 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Neman Zama Admin Ƙaro Na Biyu
[gyara masomin]| Akwai goyon baya. –Ammarpad (talk) 20:48, 15 ga Janairu, 2026 (UTC) |
Wannan tattaunawar an rufe ta. Babu buƙatar a sake ƙara wani bayani a wannan sashin. Duk wani ƙarin bayani, za'a iya yin sa shafin da ya dace ko kuma a babban shafin Kofar al'umma. Ku tuna, babu buƙatar ƙara kowane irin bayani a wannan sashin.
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh. Ina fatan kuna cikin ƙushien lafiya. Enah Wannan rubutu nawa ne domin sake gabatar da buƙatata karo na biyu na samun damar zama Admin a Hausa Wikipedia. A baya na riga na gabatar da irin wannan buƙata, kuma a wannan karo ina ƙara jaddada sha’awata da ƙudirin da nake da shi na ci gaba da yi wa Hausa Wikipedia hidima. Na dade ina ba da gudunmawa ta hanyar ƙirƙira, gyarawa da inganta muƙaloli, tare da taimakawa sababbin masu gyara su fahimci ka’idoji da tsarin aikin Wikipedia. Ina da cikakken shiri da niyyar ɗaukar nauyin da ke tattare da matsayin Admin, musamman wajen kula da muƙaloli, da dakile masu lalata muƙala, da tabbatar da ingancin bayanai a Hausa Wikipedia. Ina roƙon Editors din Hausa Wikipedia da su sake duba wannan buƙata ta tare da ni, tare da ba ni wannan dama idan sun ga na cancanta. Zan yi farin cikin karɓar duk wata shawara ko gyara da za ta taimaka wajen inganta aikina Nagode. Smshika (talk) 09:46, 29 Disamba 2025 (UTC)
- Ni Umar-askira ina mai goyon bayan ka domin zama admin a Hausa Wikipedia saboda jajurcewar ka wajen inganta rubutan Hausa a manhajar Hausa Wikipedia. Fatan Allah ya bada nasara ameen. Umar-askira (talk) 17:23, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
Support
[gyara masomin]- ina goyon baya ɗari bisa ɗari domin zai kawo cigaba sosai a Wikipedia Nnamadee (talk) 20:42, 29 Disamba 2025 (UTC)
- Ina goyon baya sosai... hakan zai kawo cigaba Captain Pharouq 20:49, 29 Disamba 2025 (UTC)
- enah goyan bayan kazama Admin karo nabiyi sabo da jajir cewanka Hauwa'u lawal ardo (talk) 21:06, 29 Disamba 2025 (UTC)
- Kasancewar ka edita mai bada gudummawa a kusan koda yaushe, ina goyon baya domin sake baka damar zai ƙara bunƙasa maƙalolin Hausa Wikipedia Mahuta (talk) 22:07, 29 Disamba 2025 (UTC)
- Ina goyon Bayan ka sake Zama admin a karo na biyu saboda jajircewar ka Hakan Zai Kara kawo cigaba sosaeAisha Yahuza (talk) 22:14, 29 Disamba 2025
- ina goyon baya ɗari bisa ɗari domin zai kawo cigaba sosai a Wikipedia domin yana kawo wa Umar A Muhammad (talk) 05:16, 30 Disamba 2025 (UTC)
- enah goyan bayanka kazama Admin karo na biyu sabo da ƙoƙarin da kake yi Asma,u Khamis hussaini (talk) 17:20, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- enah goyon bayan kazama Admin Ifteehern (talk) 17:25, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Abdulrahman tahir shika (talk) 17:29, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)ina goyon baya sosai sabida zaikawo muna cigaba sosai Abdulrahman tahir shika (talk) 17:29, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya, Allah ya bada Sa'a Gwanki(Yi Min Magana) 17:30, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- ina goyan bayan kazama admin a karo na biyu saboda jajir cewarka Fateemah usman (talk) 17:42, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyan bayan kasancewar ka a matsayin mai gudanarwa a karo na biyu a sakamakon irin jajircewa da gudummawar da kake bayarwa domin tsaftace shafin Hausa Wikipedia. A Sulaiman Z (talk) 18:22, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon bayan sake dawowar ka... Allah ya taimaka. Jidda3711 (talk) 18:30, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
Neman Admin a karo na biyu
[gyara masomin]| Akwai goyon baya –Ammarpad (talk) 20:47, 15 ga Janairu, 2026 (UTC) |
Wannan tattaunawar an rufe ta. Babu buƙatar a sake ƙara wani bayani a wannan sashin. Duk wani ƙarin bayani, za'a iya yin sa shafin da ya dace ko kuma a babban shafin Kofar al'umma. Ku tuna, babu buƙatar ƙara kowane irin bayani a wannan sashin.
Assslamu Alaikum, ina neman goyon bayanku domin kasancewa mai gudanarwa a karo na biyu domin tantance ayyuka, da kuma bada tallafi ga sabbin editoci. Saifullahi AS (talk) 10:00, 6 ga Janairu, 2026 (UTC)
Support
[gyara masomin]- Ina goyon byan hakan domin zai kawo cigaba a wikipedia Ibrahim abusufyan (talk) 18:13, 6 ga Janairu, 2026 (UTC)
- ina mai goyon bayen hakan domin hakan zai kawo cigaba gaba sosai a wikipedia Mahmud maby (talk) 21:11, 6 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Abusule dankofa (talk) 22:03, 6 ga Janairu, 2026 (UTC)ina Mai goyan bayan hakan
- ina gonyon baya dari bisa dari dan zai kawo kawo cigaba a Wikipedia Muhdavdullahi (talk) 22:06, 6 ga Janairu, 2026 (UTC)
- ina mai bada goyon baya dari bisa dari akan wannan domin zai kawo cigaba sosai. Abdoulmerlic (talk)
- Support, duba da irin gudunmawarka a ko yaushe, hakan zai kawo cigaba wajen ciyar da Hausa Wikipedia gaba. BnHamid (talk)
- Ina goyon baya Dari bisa Dari Sardeeq (talk) 11:49, 7 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya sosai.... Captain Pharouq 12:35, 7 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon bayan ɗari bisa ɗari Nnamadee (talk) 12:41, 7 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Khalifah123 (talk) Ina Goyan bayan hakan domin zaya kawo cigaba a Wikipedia Khalifah123 (talk)
- Abdulrahman tahir shika (talk) 17:24, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)ina goyon baya Dari bisa dari zaikawo muna cigaba sosai Abdulrahman tahir shika (talk) 17:24, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- ina gonyan baya dari bisa Dari kazamu admin Dan kawo cigaba a Wikipedia Fateemah usman (talk) 17:33, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya –Ammarpad (talk) 08:49, 9 ga Janairu, 2026 (UTC)
- SUPPORT...Ina goyon bayan wannan Kuduri Ibkt (talk) 13:45, 11 ga Janairu, 2026 (UTC)
Sanarwa
[gyara masomin]Muna sanar da al’ummar Hausa Wikipedia game da shirin Celebrating International Women’s Day Through The Wikimedia Projects 2026, wanda ke da nufin ƙarfafa wakilcin mata da haɓaka gudunmawar su a ayyukan Wikimedia, musamman a harshen Hausa. Muna maraba da ra’ayoyi da shawarwari daga al’umma. Sirjat (talk) 11:20, 8 ga Janairu, 2026 (UTC)
==
Logo don murnar cikar Wikipedia shekaru 25
[gyara masomin]| Akwai goyon baya. –Ammarpad (talk) 16:18, 22 ga Janairu, 2026 (UTC) |
Wannan tattaunawar an rufe ta. Babu buƙatar a sake ƙara wani bayani a wannan sashin. Duk wani ƙarin bayani, za'a iya yin sa shafin da ya dace ko kuma a babban shafin Kofar al'umma. Ku tuna, babu buƙatar ƙara kowane irin bayani a wannan sashin.

A cikin wannan watan Wikipedia ke cika shekaru ashirin da biyar da kafuwa. Inason yin amfani da wannan lokaci domin taya daukacin editocin Hausa Wikipedia murnar cikar wannan shekaru. Wannan babbar nasara ce garemu baki daya.
Saboda murnar wannan lokacin, ina son mu canza logon mu domin taya Wikipedia murna.
A nan gefe zaku iya ganin sabon hoton logon murnar, wanda aka fassara da Hausa daga logon Turanci wanda Gidauniyar Wikimedia ta bada saboda murnar zagayowar lokacin.
Idan kuna goyon bayan haka sai ku rubuta a nan ƙasa. Saifullahi AS (talk) 09:03, 10 ga Janairu, 2026 (UTC)
Support
[gyara masomin]- Ina goyon baya sosai domin taya Wikipedia murnar cika shekaru 25. Nassmart1 (talk) 18:49, 10 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya. Fatan nasara Captain Pharouq 08:49, 11 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Yayi kyau, ina goyon baya. –Ammarpad (talk) 09:00, 11 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Support ina goyon baya Ibkt (talk) 13:49, 11 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya sosai, ina kuma taya Wikipedia murnar cika shekaru 25. Gwanki(Yi Min Magana) 05:41, 15 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon Baya domin taya Wikipedia murnar cika shekara 25Muhdavdullahi (talk) 13:33, 18 ga Janairu, 2026 (UTC)
SANARWA TARE DA NEMAN GOYON BAYA
[gyara masomin]Assalamu alailum, inaso nayi amfani da wannan damar domin na shaida maku muna shirin gudanar da taron Wikipedia a jihar Niger insha Allah, wanda shirin zai bunƙasa shafukan Wikipedia da kuma yan'uwanta, sannan shirin zai bunƙasa samar da sabbin esitoci a Hausa Wikipedia. Allah ya bamu sa'a da nasara Umar A Muhammad (talk) 12:26, 11 ga Janairu, 2026 (UTC)
Neman Zama Admin A Hausa Wikipedia
[gyara masomin]Assalamu Alaikum editoci masu albarka,fatan muna cikin koshin lafiya Allah yasa haka ne amin. Ina mai amfani da wannan damar domin sanar daku da neman goyon bayanku game da kasancewa na admin a manhajar Hausa Wikipedia. In a fatan mu cigaba da kasancewa lafiya amin ya Rabbal alamin. Bissalam. Umar-askira (talk) 10:52, 13 ga Janairu, 2026 (UTC)
Support
[gyara masomin]- Ina goyon baya.. Allah ya bada Sa'a Jidda3711 (talk) 16:05, 14 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya. I support Anasysmart (talk) 07:12, 15 ga Janairu, 2026 (UTC)
- Ina goyan baya 100% ..Allah ya taimaka Saudarh2 (talk) 09:59, 15 ga Janairu, 2026 (UTC)
- enah goyon bayanka kazama Admin sbd jajircewanka a Hausa Wikipedia Smshika (talk) 10:14, 15 ga Janairu, 2026 (UTC)
Sanarwa
[gyara masomin]assalamualaikum Barka da wannan lokaci shuwagabanni da ƴan uwa na editors, Ina sanar da ku cewa zan rubuta proposal game da Local Health Knowledge for All: Building Hausa Medical Content on Wikipedia Hausaal Local Health Knowledge for All: Building Hausa Medical Content on Wikipedia Hausa. Idan akwai shawarwari ko ƙarin bayani a shirye nake da yin amfani da su. Nagode sosai. @M Bash Ne (talk) 20:22, 15 ga Janairu, 2026 (UTC)
muna goyan bayan sa saboda jajir ciwar shi Musa650 (talk) 07:19, 16 ga Janairu, 2026 (UTC)
Thank You for Last Year – Join Wiki Loves Ramadan 2026
[gyara masomin]Dear Wikimedia communities,
We hope you are doing well, and we wish you a happy New Year.
Last year, we captured light. This year, we’ll capture legacy.
In 2025, communities around the world shared the glow of Ramadan nights and the warmth of collective iftars. In 2026, Wiki Loves Ramadan is expanding, bringing more stories, more cultures, and deeper global connections across Wikimedia projects.
We invite you to explore the Wiki Loves Ramadan 2026 Meta page to learn how you can participate and sign up your community.
📷 Photo campaign on Wikimedia Commons
If you have questions about the project, please refer to the FAQs:
Early registration for updates is now open via the Event page
Stay connected and receive updates:
We look forward to collaborating with you and your community.
The Wiki Loves Ramadan 2026 Organizing Team 19:44, 16 ga Janairu, 2026 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Sanarwa da neman goyon baya
[gyara masomin]Barkann mu da wannan lokacin yan'uwana editoci, muna shirin gudanar da wani taro nan bada jimawa ba a jihar Plateau, dan haka nake sanar da ku tare da neman shawarwarin ku da kuma goyon bayan ku, Nagode Abdulmuddalib Iabrahim Salisu (talk) 20:25, 17 ga Janairu, 2026 (UTC)
Feminism and Folklore 2026 starts soon
[gyara masomin]
- Invitation to Organize Feminism and Folklore 2026
Dear Wiki Community,
We are pleased to invite Wikimedia communities, affiliates, and independent contributors to organize the Feminism and Folklore 2026 writing competition on your local Wikipedia.
The international campaign will run from 1 February to 31 March 2026 and aims to improve coverage of feminism, women’s histories, gender-related topics, and folk culture across Wikipedia projects.
- About the Campaign
Feminism and Folklore is a global writing initiative that complements the Wiki Loves Folklore photography competition. While Wiki Loves Folklore focuses on visual documentation, this writing campaign addresses the gender gap on Wikipedia by improving encyclopedic content related to folk culture and marginalized voices.
- What Can Participants Write About?
Communities can contribute by creating, expanding, or translating articles related to:
- Folk festivals, rituals, and celebrations
- Folk dances, music, and traditional performances
- Women and queer figures in folklore
- Women in mythology and oral traditions
- Women warriors, witches, and witch-hunting narratives
- Fairy tales, folk stories, and legends
- Folk games, sports, and cultural practices
Participants may work from curated article lists or generate new article suggestions using campaign tools.
- How to Sign Up as an Organizer
Organizers are requested to complete the following steps to register their community:
- Create a local project page on your wiki (see sample)
- Set up the campaign using the CampWiz tool
- Prepare a local article list and clearly mention:
- Campaign timeline
- Local and international prizes
- Request a site notice from local administrators (see sample)
- Add your local project page and CampWiz link to the Meta project page
- Campaign Tools
The Wiki Loves Folklore Tech Team has introduced tools to support organizers and participants:
- Article List Generator by Topic – Helps identify articles available on English Wikipedia but missing in your local language Wikipedia. The tool allows customized filters and provides downloadable article lists in CSV and wikitable formats.
- CampWiz – Enables communities to manage writing campaigns effectively, including jury-based evaluation. This will be the third year CampWiz is officially used for Feminism and Folklore.
Both tools are now available for use in the campaign. Click here to access the tools
- Learn More & Get Support
For detailed information about rules, timelines, and prizes, please visit the Feminism and Folklore 2026 project page.
If you have any questions or need assistance, feel free to reach out via:
- Meta talk page
- Email us using details on the contact page.
- Join Us
We look forward to your collaboration and coordination in making Feminism and Folklore 2026 a meaningful and impactful campaign for closing gender gaps and enriching folk culture content on Wikipedia.
Thank you and best wishes,
Feminism and Folklore 2026 International Team
Invitation to Host Wiki Loves Folklore 2026 in Your Country
[gyara masomin]
Hello everyone,
We are delighted to invite Wikimedia affiliates, user groups, and community organizations worldwide to participate in Wiki Loves Folklore 2026, an international initiative dedicated to documenting and celebrating folk culture across the globe.
- About Wiki Loves Folklore
Wiki Loves Folklore is an annual international photography competition hosted on Wikimedia Commons. The campaign runs from 1 February to 31 March 2026 and encourages photographers, cultural enthusiasts, and community members to contribute photographs that highlight:
- Folk traditions and rituals
- Cultural festivals and celebrations
- Traditional attire and crafts
- Performing arts, music, and dance
- Everyday practices rooted in folk heritage
Through this campaign, we aim to preserve and promote diverse folk cultures and make them freely accessible to the world.
Project page on Wikimedia Commons
- Host a Local Edition
As we celebrate the eight edition of Wiki Loves Folklore, we warmly invite communities to organize a local edition in their country or region. Hosting a local campaign is a great opportunity to:
- Increase visibility of your region’s folk culture
- Engage new contributors in your community
- Enrich Wikimedia Commons with high-quality cultural content
If your team prefers to organize the competition in either February or March only, please feel free to let us know.
If you are unable to organize, we encourage you to share this opportunity with other interested groups or organizations in your region.
- Get in Touch
If you have any questions, need support, or would like to explore collaboration opportunities, please feel free to contact us via:
- The project Talk pages
- Email: support@wikilovesfolklore.org
We are also happy to connect via an online meeting if your team would like to discuss planning or coordination in more detail.
Warm regards,
The Wiki Loves Folklore International Team
MediaWiki message delivery (talk) 13:21, 18 ga Janairu, 2026 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Bitar shekara-shekara na Universal Code of Conduct da Ka’idojin Aiwatarwa
[gyara masomin]Ina rubuto maka ne domin sanar da kai cewa an buɗe lokacin bitar shekara-shekara na Universal Code of Conduct da Ka’idojin Aiwtarwa. Kana iya ba da shawarwari kan sauye-sauye har zuwa 9 ga Fabrairu, 2026. Wannan shi ne mataki na farko cikin jerin matakai da za a ɗauka domin bitar shekara-shekara. Karanta ƙarin bayani kuma ka samu tattaunawa da za ka shiga a shafin UCoC a Meta.
The Kwamitin Daidaita Aiwatar da Universal Code of Conduct (U4C) wata ƙungiya ce ta duniya da ta sadaukar da kai wajen tabbatar da adalci da daidaitaccen aiwatar da UCoC. Wannan bitar shekara-shekara an tsara ta kuma an aiwatar da ita ne ta hannun U4C. Don samun ƙarin bayani da kuma fahimtar nauyin da ke kan U4C, kana iya duba Kundin Tsarin U4C.
Da fatan za a raba wannan bayanin zuwa ga wasu mambobi a cikin al'ummarku inda ya dace.
-- A cikin haɗin gwiwa da U4C, Keegan (WMF) (tattaunawa)
21:01, 19 ga Janairu, 2026 (UTC)
(This message was sent to Wikipedia:Community Portal and is being posted here due to a redirect.)
Sanarwa game da shirin kaddamar da project na WikiFemme Learning Lab in Bauchi
[gyara masomin]Assalamu alaikum,
Muna sanar da fara aikin WikiFemme Learning Lab In Bauchi, wani aikin Rapid Fund daga Wikimedia Community Fund da ke nufin ƙarfafa mata su shiga cikin ayyukan Wikimedia, musamman Wikipedia. Aikin zai ba da horo da tallafi don mata su koyi gyara da ƙirƙirar abubuwan ilimi, tare da rage gibi a wakilcin mata a cikin abun da ke kan Wikipedia.
Muna gayyatar al’umma su ba da shawarwari da goyon baya domin tabbatar da nasarar wannan aiki da ƙara tasirinsa a Bauchi da kewaye.
Na gode. Santa MMD (talk) 22:02, 27 ga Janairu, 2026 (UTC)
Saving the Knowledge of Endangered Hausa Expressions and Idioms Through Wikimedia Projects
[gyara masomin]Ina farin cikin sanar da ku cewa da shuwagabanni da ƴan uwa Editors na wannan manhajar cewa, zamu rubuta proposal game da "Saving the Knowledge of Endangered Hausa Expressions and Idioms Through Wikimedia Projects" muna neman goyon baya da kuma shawarwarin ku, Nagode sosai.@M Bash Ne (talk) 22:19, 29 ga Janairu, 2026 (UTC)
Lafiyar mata a shafin Hausa Wikipedia
[gyara masomin]Assalamu Alaikum sanunku da warhaka, ina shirya neman Wikimedia Rapid Fund don aiki a kan inganta **bayanan lafiyar mata a shafin Hausa Wikipedia**. Aikin, *"Bridging Women’s Health Knowledge in Hausa,"* zai ƙunshi fassara labarai masu kyau daga Wikipedia ta Ingilishi zuwa Hausa, wanda ya shafi batutuwa kamar lafiyar uwa, lafiyar haila, lafiyar haihuwa, da cututtukan da ke shafar mata. Muna kuma shirin ɗaukar nauyin horo ta hanyar intanet da kuma aikin editing don tallafawa sabbin editoci da ƙwararru wajen koyon yadda ake fassara da inganta abubuwan lafiya ta amfani da nassoshi masu inganci.
Wannan shiri zai faɗaɗa samun ingantattun bayanai game da lafiya a cikin Hausa Wikipedia musamman ga mata, sa' anan zai rage gibin ilimi da ke da alaƙa da lafiyar mata, da kuma ƙarfafa janyo sabin edtoci zuwa shiga cikin al'ummar Hausa Wikimedia. Muna maraba da ra'ayoyin al'umma kan batutuwa masu mahimmanci, sha'awar shiga a matsayin edita ko mai ba da shawara, da duk wani shawarwari da za su iya taimakawa wajen inganta wannan aiki. Ra'ayoyinku za su taimaka wajen tabbatar da cewa aikin ya cika buƙatun al'umma kuma yana da tasiri mai ma'ana. Umabruka (talk) 20:54, 1 ga Faburairu, 2026 (UTC)
Shirye shiryen taron Women and Culture Awareness in Nigeria 2026
[gyara masomin]Assalamu Alaikum ina farin cikin sanar daku cewa muna shirye shiryen gudanar da gasa da kuma taro akan wayar da kai game da Mata da kuma al'adu a Najeriya. Nassmart1 (talk) 11:26, 7 ga Faburairu, 2026 (UTC)
Neman Zama Admin A Hausa Wikipedia
[gyara masomin]Assalamu Alaikum, ina neman goyon bayanku domin kasancewa mai gudanarwa domin tantance ayyuka, da kuma bada tallafi ga sabbin editoci a wannan manhaja ta Hausa Wikipedia.Nnamadee (talk) 22:49, 7 ga Faburairu, 2026 (UTC)
Support
[gyara masomin]- Ina goyon baya sosai. Fatan nasara Captain Pharouq 23:05, 7 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- enah goyon bayan kazama Admin Smshika (talk) 04:45, 8 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- ina Mai goyon Baya Dari bisa DariMuhdavdullahi (talk) 05:08, 8 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon bayan zaman wannan ƙwararren edita ya zama admin a Hausa Wikipedia, domin ina da tabbacin zai taimaka da ƙara bunƙasa maƙalolin da ke Hausa Wikipedia tare da samar da sabbin maƙaƙolin, dan haka ina hoyon baya Mahuta (talk) 05:11, 8 ga Faburairu, 2026
- Ina Matugar Nuna goyon baya akan hakan ~2026-85864-0 (talk) Muktee1494
- ina goyon baya don inganta wikipediaIbrahim abusufyan (talk) 06:31, 8 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- Ina goyon baya don kwazo day jajircewar wannan editaAisha Yahuza (talk) 08:19, 8 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- inagoyon baya dari bisa dari Allah yataimakaSardeeq (talk) 21:36, 9 ga Faburairu, 2026 (UTC)
Wikimedia knowledge sharing in America University of Nigeria
[gyara masomin]Assalamu alaikum jama,a naxo ne domin in sanar da ku cewa na shirya wani aiki da zai wayar da kan jama'a game da harkar Wikimedia a Jami'ar Amurka ta Najeriya. Dake garin Adamawa Aikin yana da nufin wayar da kan jama'a game da ayyukan Wikimedia da horar da sabbin editoci kan yadda za su ba da gudummawa ga ayyukan Wikimedia. Ina neman goyon bayanku da shawarwarinku domin samun nasarar aikin. na gode. Baby juuu (talk) 15:16, 9 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- Sannu da kokari, amma babu cikakken bayani game da aikin dan haka bamu san wacce irin shawara zamu bayar ba. Nagode Gwanki(Yi Min Magana) 13:19, 15 ga Faburairu, 2026 (UTC)
Campaign in Diseases and Public Health in Nigeria
[gyara masomin]assalamu alaikum muna sanar maku da fara shirye shiryen campaign mai suna Diseases and Public Health in Nigeria Ibrahim abusufyan (talk) 11:00, 10 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- Wa'alaika Assalam @Ibrahim abusufyan, Ko zamu iya samun ƙarin bayani game da gangamin? Yana da kyau a rinka saka cikakken bayani saboda kada a samu hadaka wajen gudanar da irin wannan aikin. Nagode Gwanki(Yi Min Magana) 13:21, 15 ga Faburairu, 2026 (UTC)
- @Gwanki An dakatar da maganar wannan aiki sai nan gaba. Captain Pharouq 14:23, 17 ga Faburairu, 2026 (UTC)
Wiki For Indigenous Games: Documenting Traditional Hausa Games
[gyara masomin]Assalamualaikum Barka da wannan lokaci shuwagabanni da ƴan uwana editoci na wannan manhajar, ina mai sanar da ku cewa zan rubuta proposal mai taken Wiki for Indigenous Games: Documenting Traditional Hausa Games. Ina mai neman goyon bayan ku da shawarwarin ku.Nagode@Salahu Gwanki (talk) 18:39, 15 ga Faburairu, 2026 (UTC)