BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 28/02/2026
Yadda Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hari kan Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana lamarin a matsayin “babba kuma mai ci gaba,” kuma an ji fashe-fashe a biranen Iran da dama.
Mutumin da ya yanke shawarar komawa rayuwa a cikin ƙogo
Ya zauna cikin ƙogon mai nisan mita 130 na aƙalla watanni biyu shi kaɗai tare da fitila irin ta masu haƙar ma'adinai domin ya samu haske.
Falalar goman tsakiya na Azumin Ramadan
Watan Ramadan baki ɗayansa na ƙunshe da falala tun daga 10 na farko, zuwa 10 na tsakiya, da kuma kwanaki mafi daraja na 10 ta ƙarshe. Ko akwai wata falala ta musamman game da goma ta tsakiya?
'Yadda kan iyakar Najeriya da Nijar da Benin ta zama cibiyar ƴanbindiga'
Wani sabon binciken ƙungiyar da ke kula da alƙaluman wuraren da ak gudanar da rikice-rikici ta ACLED ya nuna cewa kan iayakar Najeriya da Benin da kuma Jamahuriyar Nijar na neman zama wata sabuwar cibiyar rikice-rikice a 2025.
Yadda rikicin Pakistan da Afghanistan ya samo asali
Yayin da hare-haren kan iyaka ke ƙara ta'azzara tsakanin Pakistan da Afghanistan, ko mene ne tarihin tushen tashe-tashen hankula na yanzu?
Dalilan ADC na watsi da sabon jadawalin INEC
Jam'iyyar ADC a Najeriya ta yi watsi da sabon jadawalin da hukumar zaben kasar ta fitar dangane da babban zaben kasar na 2027
Malami zai ci gaba da zama a tsare kafin cika ƙa'idar beli
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 27 ga watan Fabrairun 2026.
Ta yaya sauya ranar zaɓen 2027 zai shafi shirin jam'iyyu da ƴantakara?
A ranar Alhamis ne hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta sanya sabbin ranakun gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da na gwamnoni da kuma na majalisun jihohi na 2027.
Yaƙi ya ɓarke tsakanin Pakistan da Taliban
Jiragen yaƙin Pakistan sun kai hare-hare cikin ƙasar Afganistan, inda suka yi ruwan bama-bamai a wasu sassan Kabul da Kandahar da Paktia, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa tsakaninsu.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 28 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 28 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 28 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 27 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Wasanni
An fitar da jadawalin zagayen ƴan 16 na Gasar Champions League
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 22 zuwa 27 ga Fabrairu 2026
Man Utd da Man City na hamayya kan Anderson, ina Griezmann zai tafi?
Manchester City da Manchester United na hammaya kan ɗanwasan Nottingham Forests Elliot Anderson, Inter Milan na nazari kan ɗanwasan Liverpool Curtis Jones yayin da Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ba shi da tabbas kan makomar Antoine Griezmann.
Champions League: Madrid da City, Barca da Newcastle, Arsenal da Bayer
Za a buga fallen farko na wasannin ne ranakun 10 da kuma 11 ga watan Maris, sannan a buga falle biyu na wasannin a ranakun 17 da 18 ga watan na Maris.
Liverpool ta nace wa Murillo, darajar Osimhen ta lunka
An yi watsi da raɗe-raɗin cewa Jurgen Klopp zai bar aikinsa a Red Bull, Chelsea na kan bakarta kan land Murillo yayin da farashin da Wolves ta saka kan Mateus Mane ke neman sauya ra'ayin Liverpool da Manchester United.
Ƴan ƙwallo Musulmai da ke taka leda suna azumin Ramadan
Musulmai na gudanar da azumin Ramadana a fadin duniya, haka nan ma ƴan wasan ƙwallon ƙafa Musulmai a nahiyar Turai na ci gaba da gudanar da sana'arsu duk kuwa da cewa wajibi ne su ƙaurace wa ci da sha, kamar yadda addini ya tanada.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ku aiko mana girke-girken Ramadan na 2026
Ku sanya bidiyon abincin buɗe-baki na musamman da kuka haɗa wa iyalanku ta yadda wasu za su iya kallo su kwaikwaya.
Yadda dajin Kainji ke neman zama maɓoyar ƙungiyoyin ƴanbindiga a Najeriya
Wata fargabar da ake yi, ita ce yiwuwar dajin ya zama kamar Sambisa a nan gaba, lamarin da Kabiru Adamu ya ce akwai dalilai da ke nuna haka.
Mene ne hukuncin mai yin ƙorafi saboda azumi?
Mene ne hukuncin masu cewa 'yau azumi babu sauƙi' ko 'yau lokaci ba ya gudu'? Sheikh Aminu Daurawa ya amsa wannan tambaya.
Ko sola na iya haifar da gobara?
Samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, wanda aka fi sani da 'solar' na ci gaba da samun karɓuwa a ƙasashen Afirka masu tasowa, inda ake fama da ƙarancin lantarki.
Yadda APC da ADC ke cacar baki kan rikicin siyasar Edo
Ana ci gaba da cacar baki tsakanin APC da kuma ADC, dangane da harin 'yan bindiga da suka kai wa wasu kusoshin jam'iyyar adawar a jihar Edo
Inec ta sauya ranar zaɓen shugaban Najeriya na 2027
Hakan na zuwa ne mako biyu bayan hukumar ta fitar da jadawalin zaben na farko, wanda ya sha suka daga bangarori da dama kasancewar ranakun da hukumar ta sanar za su iya fadawa cikin watan azumin Ramadana na shekarar 2027.
Yadda mutane ke mutuwa a hannun ƴansanda saboda azaba - Amnesty
Ƙungiyar Amnesty ta ce sashen na Tiger Base na kamawa da tsare mutane, sannan azabtar da su, inda wasu ke mutuwa saboda azaba.
Gwamnatin Jigawa ta karɓi Walida Abdulhadi
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 26 ga watan Fabrairun 2026.
Yadda yaƙin Sudan ya karkata ga yanki mai arziƙin zinare da ɗanyen man fetur
Tsanantar hare-hare a yankin Kordofan ya shafi mutane masu ɗimbin yawa, yayin da har yanzu babu haske game da kawo ƙarshen yaƙin.
Matsaloli 7 da suka kamata sufeton ƴansadan Najeriya ya fara magancewa
Ganin shugaban na ƴansanda ya karɓi aiki a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsalolin tsaro daban-daban, sai wasu suke ganin tamkar ba dole ba ne a samu wani gagarumin sauyi.
Shin za a ci gaba da tsare El-Rufai har watan Afrilu, me doka ta ce?
Idan har aka keta ƴanci da ɗan kasa ke da su, za a iya kai wa wani mataki da za a iya yin watsi da batun laifin da ake tuhumarsa da shi a koma kan batun take haƙƙinsa, a cewar masanin shari'a a Najeriya.
Ko shirin nukiliyar Iran barazana ce ga duniya?
Shugaban Amurka Donald Trump na ta tura kayan yaƙi domin matsa wa Iran, wane mataki Iran take a shirinta na nukiliya bayan harin Amurka na bara?
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.


































































